Daidai ne namiji ya yi mata hudu – Sheikh Kabir Gombe

Daidai ne namiji ya yi mata hudu – Sheikh Kabir Gombe

- Sakataren kungiyar Izala ya ce Allah ne ya ba namiji damar auran mata dai-dai har hudu

- A cewar Kabiru Gombe kusa a kasashen duniya mata sunfi maza yawa

Babban sakataren kungiyar nan ta addinin musulunci mai suna Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Kabiru Gombe, ya jaddada cewa Allah madaukakin sarki ne ya halartawa maza auran mata guda dai-dai har hudu.

Shehin malamin ya bayyana ne a yayin wata hira da yayi da shafin BBC a dake birnin Landan.

Daidai ne namiji ya yi mata hudu – Sheikh Kabir Gombe
Daidai ne namiji ya yi mata hudu – Sheikh Kabir Gombe

A cewar Kabiru Gombe, a halin yanzu mata sun fi maza yawa a kusan dukkannin kasashen duniya.

KU KARANTA KUMA: Sanatoci sun aikawa wani babban Jami’in Gwamnatin Tarayya goron gayyata

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kabiru ya bayyana cewa ya fuskanci cewa an bar iyayen namu matan ne a baya musamman ma ta fuskar wa'azi da sauran al'amurran addinin musulunci baki daya shiyasa ya fi karkata wajen yi masu wa’azi.

Ya kuma jaddada cewa tabbas wa'azantar da 'ya'ya matan yafi na mazan muhimmanci domin suma tamkar wata makaranta ce sukutum a cikin gidajen su da kuma 'ya'yan da suka haifa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng