Na siya bindiga kirar AK 47 kan kudi naira 470,000: Barawon shanu ya fadawa 'yan sanda
- Rundunar yan sanda reshen Jihar Katsina tayi nasarar cafke gawurtatun 'yan fashi
- Cikin wanda aka cafke harda wani matashi wanda ya shaida wa 'yan sandan cewa ya siya bindigar kirar AK 47 kan kudi naira 470,000
- Umar ya kashe mutane da dama a yayinda suke gudanar da fashi da satan shanu tare da sauran 'yan uwansa
Rundunar 'yan sandan Jihar Katsina tayi nasarar damke wani barawon shanu kuma mai fashi da makami dan shekaru 25 mai suna Ibrahim Umar, Umar ya shaida wa 'yan sandan cewa ya siya bindigar sa kirar AK 47 kan kudi naira 470,000.
Umar wanda aka fi sani da Oro mazaunin kauyen Yankuzo ne da ke karamar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Yana daya daga cikin mutane 17 da rundunar ta cafke bisa zargin aikata laifufuka da dama kuma aka tsare su a hedkwatan rundunar da ke Katsina.
KU KARANTA: APC reshen Kano ta yi barazanar kai Buhari kara a kotu idan ya ki fitowa takara karo na 2
Ya shaida wa jaridar Northern City cewa ya siya bindigar AK 47 din ne a dokan daji amma ba zai iya gane mutumin da ya siyar masa da bindigar ba.
Kwamishinan rundunar 'yan sandan Jihar Katsina, Besen Gwana yace Umar ya amsa cewa yana cikin wata kungiyar 'yan fashi tare da wasu mutane 14 da suka dade suna adabar al'umma a jihohin Katsina da Zamfara.
Umar wanda ya nuna kwarewa wajen amfani da bindigar ya fadawa yan sanda cewa ya kashe mutane da dama a yayinda suke gudanar da fashi ko satan shanu.
Hakazalika, ya kashe 'yan uwansa guda 2, Haladu Rabiu da Rabiu Yahaya bisa kuskure lokacin da yake amfani da bindigar. Za'a gurfanar da Umar gaban kotu bayan an kamala bincike.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng