Abin da ya sa ake kira na Shu'uma — Fati
Shararriyar jarumar nan ta dandalin shirya fina-finan Hausa wato annywood, Fati Abubakar wacce aka fi sani da Fati Shu’uma ta bayyana dalilin da yasa ake kiranta da wannan suna.
A cewar jarumar, rashin jin da ta nuna a cikin fim din Shu’uma ne ya sa ake mata inkiya da wannan suna.
Fati ta bayyana cewa ta koyi tarin darasi kan makomar mutane masu munanan dabi’u a cikin wannan fim din.
Ta kuma jadadda cewa tana matukar jin dadin fitowa a matsayin muguwa cikin fina-finai.
Ta ce: "Na fi so na fito a matsayin muguwa saboda na fadakar da mutane irin illar mugunta da son rai.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa bai kamata Buhari yayi zancen dawowa na biyu ba a yanzu – Sage Africa
"Ka san yawancin jarumai sun fi son fitowa a matsayin masu kirki, amma ina ganin hakan ba ya aikewa da sako kai tsaye kamar jarumi mugu, wanda ake nuna karshensa bai yi kyau ba", in ji jarumar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng