Barayin shanu na ci gaba da tarwatsa mutane a kauyukan Zamfara
Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa har yanzu barayin shanu na ci gaba da addaban al’umman jihar Zamfara.
Wadannan yan fashi sun tarwatsa al'ummar dake zaune Kauyuka a jihar Zamfara, sannan kuma suke dora kudin jinga ga mutanen kauyukan a matsayin fansar kansu.
A yanzu haka yan gudun hijira sun yadu a kowane lungu da sako na garin Shinkafi, sun kuma kasance mata da maza inda suke neman tudun dafawa.
KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
A halin da ake ciki Sufeto janar nay an sanda ya ba da umurnin tura jami’an tsaro kauyukan domin suyi magananin yan fashin da suka damu mutanen jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng