Nagari Nakowa: Kalli kyawawan hotunan Buhari sanye da kayan kabilar Ibo

Nagari Nakowa: Kalli kyawawan hotunan Buhari sanye da kayan kabilar Ibo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu kyakkyawar tarba daga gwamnan jihar Ebonyi, tare da Sarakunan gargajiyar dake jihar da kuma sauran jiga jigan yayan jihar.

Cikin karramawar da aka yi ma Buhari, an shirya masa taron girmamawa, a filin wasa na PA Ngele dake garin Abakaliki, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Jami’an Yansanda sun halaka wasu masu garkuwa da mutane a Kaduna

Ga hotunan taron karramawar nan kama yadda Buhari Sallau ya kawo su:

Nagari Nakowa: Kalli kyawawan hotunan Buhari sanye da kayan kabilar Ibo
Buhari sanye da kayan kabilar Ibo

A wani labarin kuma, shugaba Buhari ya kaddamar da wata hanya da gwamnan jihar Umahi ya gina, mai tsayin kilomita 14.5, tare da kaddamar da hanyar sama data shiga har cikin kamaru.

Nagari Nakowa: Kalli kyawawan hotunan Buhari sanye da kayan kabilar Ibo
Buhari sanye da kayan kabilar Ibo

Daga karshe, Buhari ya yaba ma gwamnan jihar saboda irin kokarin dayake yi, sa’annan ya gode ma Sarakunan gargajiya bisa sarauta da suka nada masa.

Nagari Nakowa: Kalli kyawawan hotunan Buhari sanye da kayan kabilar Ibo
Buhari

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng