Dandalin Kannywood: Barayi sun haura gidan jarumi Suleiman Bosho

Dandalin Kannywood: Barayi sun haura gidan jarumi Suleiman Bosho

Labaran da muke samu daga masana'antar Kannywood na nuni da cewa wasu bata garin mutane sun haura a gidan fitaccen jarumin fina-finan Hausa musamman ma a fagen barkwanci watau Suleiman Bosho.

Haka ma dai kamar yadda muka samu daga majiyar ta mu wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar Asabar din da ta gabata amma sai dai mun samu tabbacin cewa barayin ba su samu nasarar daukar wani muhimmin abu ba mai anfani sosai daga gidan.

Dandalin Kannywood: Barayi sun haura gidan jarumi Suleiman Bosho
Dandalin Kannywood: Barayi sun haura gidan jarumi Suleiman Bosho

KU KARANTA: Bana sha'awar yin fim - Mansura Isa

Legit.ng ta samu dai cewa barayin da zuwa yanzu bamu san adadin yawan su ba sun haura ne cikin gidan da dare kuma suka shiga wani daki suka hargitsa shi da nufin su samu abun da suke so amma sai ba su samu ba.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ma dai mun kawo maku labarin cewa jarumin ya koka da yadda a kullu yaumin yake ta kara samun masu yi masa bakin ciki da hassada da ma a wasu lokuttan kage.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng