Kiwon Lafiya: Fa'idoji guda 9 na man ridi

Kiwon Lafiya: Fa'idoji guda 9 na man ridi

Sanin kowa ne dai ridi abu ne mai arha, toh haka shi ma man ridin. Sai dai man ridin bai kai ridin shahara ba don ba kowa ya san akwai shi ba.

Man ridi yana dauke da bitamins da minerals da wasu sinadarai na kara lafiya masu dimbin yawa. Tirkashi, wannan shi ne fa ga arha ga biyan bukata! Don haka ya dace mu yawaita yin amfani da man ridi don ribantar amfaninsa.

Kiwon Lafiya: Fa'idoji guda 9 na man ridi
Kiwon Lafiya: Fa'idoji guda 9 na man ridi

Sai dai kuma akwai wasu kwayoyin magani na lafiyar jini da basu tarayya da man ridi. Don haka mai shan wani maganin asibiti ya tabbata ya sanar da likitan shi game da man ridi da yake amfani da shi don gudun kar a ba shi wata kwayar da zata hadu da man ta haifar da wata cikas din ta dabam.

Ga dai fa'idoji kamar haka:

1) Lafiyar Gashi/Suma

Yana kara lafiyar gashi da ta fatar kai. Yana kuma rage yawan kakkabar gashin sannan yana hana kodewa ko dusashewar kalan gashi.

2) Lafiyar Fata

Man ridi ya na sa taushi da sulbin fata. Ya na kuma kare fata daga daukan kwayoyin cuta.

3) Lafiyar Zuciya

Man ridi ya na inganta lafiyar zuciya. Kaman sauran nau'o'in mai, shi ma ya na dauke da bitamins da minerala da sinadarai masu karawa zuciya lafiya.

4) Kwarin Kashi

Man ridi na dauke da sinadirai masu sa kwarin kashi. Man kuma yana hanzarta warakar kashin da ta samu matsala.

5) Magance Kunci da Damuwa

Man ridi na dauke da sinadarin da ke farkar da enzayem na cikin kwakwalws mai haifar da fara'a da walwala. Don haka man ridi na maganin kunci da damuwa.

6) Lafiyar Hakora

Kurkure baki da man ridi yana kara haske da kwarin hakora. Yana kuma kare hakora daga kwayoyin cuta.

DUBA WANNAN: Buhari zaiyi sulhu tsakanin Baru da Kachikwu, Inji shugaban VON

7) Magance Cutar Daji

Man ridi na duake da mineral da sinadarai masu magance cutar daji.

8) Karin Kuzari

Man ridi yana inganta kai-komon jini a jiki wanda hakan ke karo kuzari.

9) Magance Kumburi

Man ridi na hana kumburi a ko ina a jiki. Ya na kuma magance kumburin da ya riga ya faru.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164