Biyafara: Abubuwa na kara sukurkucewa Nnamdi Kanu
- Nnamdi Kanu yana ganin ta kan-sa yayin da Sojoji su ka taso sa gaba
- Yanzu haka ana tunani Nnamdi Kanu ya tsere ba a san inda yake ba
- Gwamnatin kasar ta sa kafar wando daya da jagoran na Kungiyar IPOB
Bisa dukkan alamu dai jagoran Kungiyar IPOB ta Biyafara Mazi Nnamdi Kanu ya tsere ba a san inda yake ba a halin yanzu.
A Ranar Juma’a ne Rundunar Sojin kasar ta sa Kungiyar da Nnamdi Kanu yake jagoranta cikin ‘Yan ta’adda bayan sun yi fito-na-fito da Jami’an tsaro kuma aka shiga neman sa ruwa a jallo a cikin gidan sa da ke Garin Aba.
KU KARANTA: Shugaba Buhari zai gana da Trump
Haka ma dai wasu matasa a Garin Umuahia sun rubuta takarda inda su ka nemi Gwamnan Jihar na Abia ya tsige Mahaifin Nnamdi Kanu wanda ke rike da sarauta a kasar. Majalisar Dattawa ita ma tace za tayi bincike game da lamarin inda ta ke ganin bai dace a jibga Sojoji a Yankin ba.
Daga baya za ku ji cewa qani daga cikin masu taimakawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi magana game da Nnamdi Kanu yace babu wanda ya isa yace zai raba Najeriya Inji Hadimin Shugaba Buhari
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ko ya dace a cire Sojoji daga Kasar Ibo?
Asali: Legit.ng