Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisa (hotuna)
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisa a yau Laraba, 13 ga watan Agusta.
Taron ya samu halartan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, da kuma manyan yan majalisa irin su mukaddashiyar babban sakatariyar tarayya Misis Habibat Lawal.
Sauran yan majalisar sun hada da shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Abba Kyari, gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele, ministan wasanni Solomon Dalung da kuma shugaban masu hidima na tarayya Misis Winifred Eyo-Ita.
Har ila yau ministar harkokin mata da ci gaban jama’a, Sanata Aisha Alhassan ta halarci zaman inda ta samu kyakkyawar tarb daga sauran ministoci da suka halarci zaman sabanin yadda ake tunanin ministocin za su juya mata baya bisa ikirarin da ta yi na nuna goyon bayanta ga takarar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Aisha Alhassan ta iso Aso Rock don zaman majalisa
Ga sauran hotunan a kasa:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng