Abin duniya da yawa: Wani mutumi ya auri bera a Kasar India

Abin duniya da yawa: Wani mutumi ya auri bera a Kasar India

- A Kasar India wani ya auri bera bayan mutuwar matar sa

- Mista Basu yana ganin matar sa ce ta dawo a jikin bera

- Bawan Allan ya rasa matar sa ne a hadarin mota kwanaki

Mun samu labari na musamman cewa wani ya auri bera bayan mutuwar matar sa a can kasar India.

Abin duniya da yawa: Wani mutumi ya auri bera a Kasar India
Wani Hindu ya auri bera a Kasar India

Wani mutumi mai suna Chidhatma Basu ya auri macen bera a Garin Bangalore na Kasar India bayan mai dakin sa ta rasu a farkon shekarar nan a wani hadarin mota. Mutuwar ta sa wannan mutumi mai shekaru 41 da 'ya 'ya 4 ya zama gwauro.

KU KARANTA: Wani Bature yayi hawan Sallah a Najeriya

Mista Basu yace wata rana yana zaune cikin takaici da maraici sai ga shi ya ga wata bera mai idanuwa da hanci sak na marigayiyar matar sa. Mutumin yace ya fahimci cewa matar sa ce kurum ta dawo daga irin abincin da take ci. Malamin da ya daura auren yace tabbas haka aka yi.

Idan ba a manta ba bayan dawowar Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari sai daga gida yake aiki a wani ofishin sa saboda beraye sun fatattake sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Beraye sun addabi Shugaban Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: