Labari cikin Hotuna: Gawar Danbaba Suntai ta isa makwanci, masoya cike da hawaye
Misalin karfe 7 na safiyar yau ne gawar tsohon gwamnan jihar Taraba, marigayi Danbaba Suntai ta iso filin tashin jirgin sama a garin Jalingo. Cikin wadanda suka tarbi gawar cikin hawaye har da gwamnan jihar Taraba mai ci yanzu Arc. Darius D. Ishaku, Maitaimakin gwamna Haruna manu, kakakin majalisan jiha Rt Hon. Abel Diah da kuma wasu manyan jami'an gwamnati da kuma dimbin masoya daga jihar har ma da baki.
DUBA WANNAN: Farfesa Osinbajo ya shilla kasar Rwanda, ko hannun wa ya bar mu?
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng