Annoba ta afkawa Kasar Sierra Leone inda daruruwa ke mutuwa

Annoba ta afkawa Kasar Sierra Leone inda daruruwa ke mutuwa

- Wata annoba ta afkawa Kasar Sierra Leone

- Yanzu haka daruruwan mutane ke ta mutuwa

- Wasu da dama kuma dai ba a san inda su ke ba

Annoba ta afkawa Kasar Sierra Leone ta nan Afrika inda aka yi rashin mutane rututu a sanadiyar wasu mulmulallun laka.

Annoba ta afkawa Kasar Sierra Leone inda daruruwa ke mutuwa
Annoba ta afkawa Sierra Leone

Wata annoba ce ta shiga Kasar inda laka ke dankarewa ta taru ta kuma toshe hanyoyin da ke kan gangare. Fiye sa mutane 245 aka rasa ta sanadiyyar wannan annoba. Rahotanni na zuwa cewa daruruwan Jama'a dai ba a san inda su ke ba.

KU KARANTA: An kashe wani da sunan sata

Annoba ta afkawa Kasar Sierra Leone inda daruruwa ke mutuwa
Wasu mutanen Sierra Leone sun bace

Kasar dai na fama da abin takaici iri-iri. Kwanakin baya cutar nan ta Ebola mai mugun yaduwa ta barke a can inda aka rasa da dama. Kasar ta kuma yi fama da rikici iri dabam na yaki kamar dai wasu kasashen na Afrika. Yanzu haka dai kasar na bukatar addua.

Ko ku na da labari cewa Tsohon Shugaban kasar Amurka watau Barrack Obama ya bar tarihi a kafafen yada labarai na zamani bayan ya daura wani hoto a shafin Tuwita.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An nemi a make masu zanga-zanga

Asali: Legit.ng

Online view pixel