Rarara ya caccaki tsohon Gwamna Kwankwaso a wakar sa
- Rarara ya kara sukar tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso
- Mawakin yace da sake wajen mutanen Kano a 2019
- Yace shi kuma Gwamnan Kano Ganduje zai yi tazarce
A sabuwar wakar Dauda Kahutu watau Rarara ya kara sukar tsohon Gwamnan Kano Injiniya Rabiu Kwankwaso.
Fitaccen Mawakin siyasar yace da sake wajen mutanen Kano a zaben 2019 don kuwa sai an darje wajen zaben Sanatan tsakiya na Jihar Kano watau mazabar da tsohon Gwamna Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso yake wakilta. Kwanan nan wakar ta 'Sannu sa sauka Dattijo' ta fito.
KU KARANTA: An kona gidan Rarara bayan ya zagi Kwakwaso
Rarara yace shi kuma Gwamnan Abdullahi Ganduje sai yayi tazarce shekaru 8 ba kakkautawa. Mawakin yace Rabiu Kwankwaso ya shigo gonar Gwamna Dr. Ganduje. Ko da dai bai kira suna ba kiri-kiri amma ba shakka da tsohon Gwamna yake kamar yadda ya saba.
Mu na samun labari cewa Alhaji Atiku Abubakar ya fara kus-kus da Jam'iyyar adawa ta PDP game da 2019. Jigon na APC a halin yanzu yana nema takarar Shugaban kasa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Dubi yadda Ganduje ke gyara Kano
Asali: Legit.ng