Kowa ya tuna bara, ba ji daɗin bana ba: Hotunan tsofaffin jiragen sama na Najeriya

Kowa ya tuna bara, ba ji daɗin bana ba: Hotunan tsofaffin jiragen sama na Najeriya

- Tuna baya shine roko, hotuna jiragen Najeriya a baya can

- Zuwa yanzu gwamnati na kokarin dawo da wannan jirage

An samar da kamfanin jiragen sama na kasa wato Nigeria Airwaysa ne a shekarar 1958 da sunan kamfanin jiragen sama da yammacin Afirka, wato West African Airwaysa Corporation, WAAC.

A shekarar 1971 ne aka canza masa suna zuwa Nigeria Airways, inda ya cigaba da amfani da wannan suna har zuwa shekarar 2003, kamar yadda Legit.ng ta samu rahoto.

KU KARANTA: Dalibai a Jigawa na ɗaukan darasi a wata makarantar Firamari da ruwa ya malale ta gaba ɗaya(Hotuna)

Da farkon kamfanin, gwamnatin Najeriya na da kaso 51 da daya ne a cikin hannun jarin kamfanin, daga bisani kuma ta mamaye kamfanin ya hanyar amshe shi gaba daya, da haka ne ya zama cikakken kamfanin jiragen Najeriya.

Kowa ya tuna bara, ba ji daɗin bana ba: Hotunan tsofaffin jiragen sama na Najeriya
Jirgin sama na Najeriya

A wancan lokaci, kamfanin na da sama da jirage guda 30, kuma yana gudanar da aikinsa ne daga filin sauka da tashin jirage na Murtala Muhammed dake Legas, kasashen da yafi zuwa sun hada da Turai, Amurka, da Saudi Arabia.

Kowa ya tuna bara, ba ji daɗin bana ba: Hotunan tsofaffin jiragen sama na Najeriya
Tikitin jirgi da ma'aikatan

Amma kash! Abinka da halayayyar yan Najeriya na almundahana da rashawa, sai da aka dukar da kamfanin sakamakon satar kudaden kamfanin da kuma cika ta da ma’aikatan da basu da aikin yi, da haka har kamfanin ta mutu a shekarar 2003.

Kowa ya tuna bara, ba ji daɗin bana ba: Hotunan tsofaffin jiragen sama na Najeriya
Jakar da ake raba fasinjojin jirgi

Sai dai gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauki gabarar dawo da kamfanin jiragen sama na kasa, kamar yadda ministan sufurin jirgin sama, Hadi Sirika ya bayyana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Kalli yadda jirgin sama ke aman wuta:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: