Kungiyar Izala za ta yi gagarumin taron bude gidan baki mallakarta a Abuja

Kungiyar Izala za ta yi gagarumin taron bude gidan baki mallakarta a Abuja

Kungiyar Izalatil bid’a wa ikamattu sunnah na gayyatar ‘yan uwa Musulmai zuwa wajen kaddamar da sabon gidan baki da ta gina mallakarta a bababn birnin Tarayya, Abuja.

Gidan ya kasance katafare mai manyan falo guda hudu da dakunan alfarma guda 20, sannan an kashe kudi kimanin N2,15,000.000.00 wajen gina shi.

A cewar rahotanni an harhada kudin ne ta hanyar fatan layyana na shekara biyu da mabiya kungiyar suka harhada a fadin Najeriya da kuma tallafi daga wasu daidaikun mutane.

Tuni dai aka sanya ma gidan suna wato ‘Gidan Shekh Abubakar Mahmud Gumi Jibwis Guest House’ wanda ke unguwar Life Camp birnin Abuja.

Gidan na dauke ne da sassa guda hudu, inda aka sanya wa ko wani sashi suna.

Kungiyar Izala za ta yi gagarumin taron bude gidan baki mallakarta a Abuja
Kungiyar Izala za ta yi gagarumin taron bude gidan baki mallakarta a Abuja Hoto: Arewablog.com

Dan haka shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau yake gayyatar ‘ya’yan kungiyar a cikin Najeriya da su halarci taron bude sabon gidan saboda su ga amfanin abubuwan da suke tarawa.

KU KARANTA KUMA: Jirgin Shugaban kasa Buhari na nan inda aka ajiye shi har gobe

Za’a gudanar da taron bude gidan ne a ranar 5-August-2017. Da misalin karfe 10:00 na safe.

A cewar Arewablog.com shugaban na Izala ya bada sanarwar cewa, duk wanda zaizo wajen bude sabon gida to ya taho da gudunmawar Naira dubu daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng