Jihar Kaduna ta kafa tarihi, ta ƙirƙiro sabon salon gudanar da zaɓe, Karanta
- Hukumar zabe zata fara gudanar da zabe da na'ura mai kwakwalwa
- Jihar Kaduna ce zata zama ta farko wajen samar da wannan na'ura
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kaduna tayi bajakolin sabon na’urar zabe da take shirin amfani da ita don gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar Litinin 10 ga watan Yuli.
Shugaban hukuma Dakta Binta Dikko Audu ne tayi wannan bajakolin na’aura a fadar gwamnatin jihar Kaduna yayi da ake gabatar da zaman majalisar zartarwa jihar karkashin jagorancin gwamna Nasiru El-Rufai.
KU KARANTA: El-Rufai: Gwamnan jihar Kaduna ko Baban yara? Kalli haɗuwarsa da wasu yara (HOTUNA)
Binta Dikko ta bayyana cewa sabon na’aurar zaben zai tabbatar da ingancin zabe, bugu da kari, na’urar zata lalata duk wani kuri’an da ba’a dangwala shi yadda ya dace ba, sa’anna kuma tana kirga kuri’u da sauri.
Legit.ng ta ruwaito wannan na’aura zabe na amfani da batir, kuma batir din na kwashe awanni 16 bai kare ba, sa’annan gaba daya nauyinsa kilo bai wuce kilo 10 ba, don haka za’a iya yawo da shi.
A yanzu haka, inji Binta, kasashe kamar su Venezuela, USA, Philippines, Namibia, Mexico, Haiti, Curaçao, Belgium, Bolivia, da Brazil.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja yana aiki:
Asali: Legit.ng