Siyasa: Matsalolin da Jam’iyyar APC ke fama da su
– A cikin makon nan ne Gwamnatin Buhari ta shekara biyu da kafuwa
– Sai dai har yanzu Jam’iyyar APC ba ta samu alkibla ba
– Kamar dai PDP, Jam’iyyar mai mulki tana cikin rikici
Jam’iyyar APC na fama ta zama Jam’iyya mai mulki tun kafuwar Gwamnati
Shugaban Jam’iyyar ya bayyana cewa ba haka su ka so ba
Ko daga ina aka samu matsala a Jam’iyyar? Ga kadan daga cikin namu tunanin
KU KARANTA: Ana jiran Buhari ya warke domin taron APC
1. Rashin kudi
Jam’iyyar APC na fama da matsalar rashin kudi tun bayan hawan Shugaba Buhari mulki wanda ya toshe duk wata kafa da Jam’iyar za ta rika tatsa daga Gwamnatin Tarayya.
2. Nadin Shugaban kasa
Shugaban Jam’iyyar Cif John Oyegun ya bayyana cewa Jam’iyyar ba ta jin dadin irin nadin da Shugaban kasa yake yi. Mafi yawanci ba a tuntubar Jam’iyya da ‘Ya ‘yan ta. Sannan kuma har yanzu ‘Yan PDP na nan rututu cikin wannan Gwamnati rike da matsayi ba a sauya su ba.
KU KARANTA: Arewa ta yaba da kamun ludayin Buhari
3. Rikicin Majalisa da sauran na cikin gida
Tun wajen nadin Shugabannin Majalisa Jam’iyyar APC ta fara dabawa kan ta wuka a ciki. Yanzu dai kusan aikin gama ya gama don kuwa ana yi wa juna kallon doya da manja ne.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Osinbajo ya karbi ragamar mulkin kasar
Asali: Legit.ng