Wasanni: Messi da Iniesta sun ci kofi 30 a Barcelona

Wasanni: Messi da Iniesta sun ci kofi 30 a Barcelona

- Lionel Messi da Andres Iniesta sun lashe kofi na 30 kowannensu a Barcelona, bayan da suka lashe Copa del Rey a ranar Asabar.

- Barcelona ta lashe Copa del Rey na bana kuma na uku a jere, bayan da ta doke Deportivo Alaves da ci 3-1, wanda hakan ya sa ta dauke shi sau 29 jumulla.

Lionel Messi da Andres Iniesta sun lashe kofi na 30 kowannensu a Barcelona, bayan da suka lashe Copa del Rey a ranar Asabar.

Barcelona ta lashe Copa del Rey na bana kuma na uku a jere, bayan da ta doke Deportivo Alaves da ci 3-1, wanda hakan ya sa ta dauke shi sau 29 jumulla.

Legit.ng ta samu labarin cewa Messi da Iniesta sun dauki kofin La Liga takwas da Spanish Super Cup bakwai da kofin Zakarun Turai hudu da Copa del Rey biyar da European Super Cup uku da kofin zakarun nahiyoyin duniya uku a Barca.

Wasanni: Messi da Iniesta sun ci kofi 30 a Barcelona
Wasanni: Messi da Iniesta sun ci kofi 30 a Barcelona

Jumulla 'yan wasa hudu ne da suka kara a fafatawar karshen a ranar Asabar suka dauki Copa del Rey sau biyar-biyar da suka hada da Lionel Messi da Andre Iniesta da Gerard Pique da kuma Sergio Busquets.

'Yan wasan hudu a Barcelona sun dauki kofin a shekarar 2009 da 2012 da 2015 da 2016 da kuma 2017.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel