Hanyoyi 6 na gane jabun kwai
Da yiwuwan ta samu labarin cewa an fara jabun shinkafa da nama. Yanzu kuma wata sabuwa ta fito, jabun shinkafa.
Mun samu rahoton cewa anayin jabun kwan kaji yanzu kuma mutane suna ci ba tare da sani ba.
Game da rahotanni, ana yin jabun kwan kajin ne da sinadarin calcium carbonate, paraffin wax da gypsum powder.
Game da masana, hada jabun kwai da sinadarai ba abu mai wuya bane. Matsalan shine akwai sinadarin Benzoic Acid da Mercury da ake amfani da shi wanda ke lalata koda kuma kan iya jan ciwon daji.
Ga hanyoyi 7 na gane jabun kwai:
1. Bawon shin a da kyali fiye da asalin kwan kaza
2. Idan ta taba shi, bai da tsantsi Kaman ainihin kwai, yanada kurzuna-kurzuna
KU KARANTA: Najeriya ta kirkiro maganin farfadiya
3. Ka girgiza kwan kafin ka fasa. Idan kaji kara a ciki ( kamar ruwa), toh jabu ne.
4. Idan jabun kwai ne, kwaiduwan da ruwan kwan zai garwayu kana fasa shi cikin kwano.
5. Warinsu ya banbanta
6. Idan ka kona bawon jabun kwan, zai kama da wuta kuma yayi warin roba
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng