Ka ji abin da ya faru da Bukola Saraki a Kauran-Namoda
– An kara nadawa Bukola Saraki sarautar gargajiya
– Shugaban Majalisar datttawar ya zama Dan Iyan Kauran Namoda
– Sarkin Kauran Namoda ya jinjinawa Bukola Saraki
Legit.ng na da labarin cewa an nada Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Abubakar Bukola Saraki a matsayin Dan Iyan Kauran Namoda jiya. Kwanaki ne kuma aka nada Turakin Ilorin din a matsayin Baba Addini.
Wannan ya faru ne lokacin da shugaban Majalisar ya isa Jihar Zamfara domin daurin auren ‘ya ‘yan Sanata Tijjani Kaura da aka yi a fadar Sarkin Kauran Namoda. Alhaji Muhammad Asha ya nada Bukola Saraki inda yace ya cancanta.
KU KARANTA: 'Yan Arewa sun yi kaca-kaca da Buhari
Haka kuma dai kwanan nan aka nada mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin Jagaban na Kasar Adamawa a lokacin da ya leka Jihar doin ya kaddamar da wasu kwangiloli.
A makon jiya Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Abubakar Bukola Saraki ya nemi mutanen Najeriya su kara hakuri su kuma cigaba da marawa Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari baya lokacin da ya je gida Ilorin.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Kwarori na shan wahala a Najeriya
Asali: Legit.ng