Tarihin Hausawa na Bayajidda na da alamar tambaya - Masana
Shugaban Jami'ar Koyo daga gida ta Najeriya, NOUN, farfesa Abdallah Uba Adamu, ya ce, tarihin Hausawa da wasu ke dangantawa da Bayajidda shafcin gizo ne.
Ya kuma ce duk mutumin da ba shi da alaka da garuruwa guda bakwai da ke arewacin Najeriya, to ba Bahaushe ba ne. Sai dai a kira shi mai magana da yaren Hausa.
KU KARANTA: An fallasa wani lauyan karya a Kano
Legit.ng ta samu labarin cewa Garuruwan dai su ne birnin Kano da Katsina da Daura da Zazzau da Rano da Gobir da kuma Biram.
Farfesa Abdallah ya kuma yi watsi da batun da wasu manazarta ke fadi cewa Hausa yare ne ba kabila ba, a inda ya ce Hausawa na da daulolinsu.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Kun ga kayataccen jirgin kasan Najeriya kuwa?
Asali: Legit.ng