Nasir El-Rufa’i ya aika sako mai zafi ga Buhari
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El Rufa’I ta aika wata zazzafan sako ga shugaba Muhammadu Buhari inda yake bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta tsananta rayuwan mutane ta hanyar rashin daukan matakai na kwarai a lokutan da yakamata.
Game da cewar jaridar Sahara Reporters, gwamnan ya bayyana wannan ne cikin wata sako da ya aikawa Buhari a watan Satumban 2016, inda yace “a cikin takaici , shugaban kasa, gwamnatinmu ta APC bata cika alkawurranta da ta yiwa mutanen kasa ba kuma ta gaza yin wasu abubuwan da yakamata a shugabanci sabanin yakin Boko Haram da rashawa."
KU KARANTA: Yan sanda dubunnai sun samu cigaba
Daga cikin abinda ya fada a cikin sakon, yace “ Shugaban ma’aikatanka kidahumi ne akan harkokin APC da kuma siyasan cikin APC saboda bai cikin wadanda suka kafata kuma bait aba takara ba a firamare, baiyi kamfe be, ko zabe.”
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng