Daka karshe, an canza sunan garin nan mai sunan batsa a jihar Katsina
Bakin jama’ a a kafofin sada zumunta da ra’ayi na yanar gizo ya tilasta karamar hukumar Kafur na jihaar Katsina su canza sunan kauyen, Masu gindi.
Shugaban karamar hukumar Kafur, Hamzz Umar, ya nada kwamiti domin neman sabon sunan da za’a sanya wa garin.
Daga karshe, sun amince su sanya mata suna, Sabon Garin Nasarawa, bayan sun kwashe kwanaki suna muhawara.
KU KARANTA: Adadin musulman duniya zai wuce na Kirista ba da dadewa ba
Kauyen dake nan tsakanin Sabuwar Kasa da Kafur, ta janyo abin Magana a cikin mutane, har wadansu ma suna zuwa daukan hoto a wurin.
Jaridar Daily Nigerian ta tattaro cewa an sanyawa garin una Masu Gindi ne saboda wani alatun dawaki mai suna ‘ Gindi, wanda yan garin suka shahara da yi.
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng