Ikon Allah: Makaho ya zama Malamin Makaranta

Ikon Allah: Makaho ya zama Malamin Makaranta

– Wani maras ido ya zama Malamin makaranta a Maiduguri

– Mustafa yace yana so ya zama Makahon Farfesa

– Yanzu haka dai wannan mutumi yana koyar da Daliban Sakandare

Ikon Allah: Makaho ya zama Malamin Makaranta
Ikon Allah: Makaho ya zama Malamin Makaranta

Wani abin al’ajabi ya faru a Jihar Borno yayin da aka dauki wani makaho daga Garin Shehuri a matsayin malamin makaranta kamar yadda muka samu labari daga Jaridar Vanguard ta kasa.

A Ranar Litinin din jiya dai Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ya dauki wani makaho mai suna Mohammed Mustafa a matsayin malamin makarantar Sakandare a Jihar. Wannan makahon dai ya roki gwamnati ta taimaka masa da aikin yi ta Rediyon BBC Hausa kwanaki. Gwamnan kuma ya cika masa burin sa, yanzu haka Mohammed yace aure zai yi.

KU KARANTA: Kiristoci na tayi wa Buhari addu'a

Gwamnan dai ya ji tausayin wannan makaho don haka ya tura sa Ma’aikatar ilmi domin a basa aikin koyarwa. Mustafa ya yi Digiri a fannin tarihi a Jami’ar Jihar Gombe, inda ya fita da sakamako na 2’2. Wannan makaho dai yace yana so ya zama Farfesa nan gaba.

A Jihar Katsina kuma mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Kiristoci ne suka shiga addu’o’i dare da rana domin Ubangiji ya ba shugaban kasar lafiya. Shugaban kasar dai yace babu dalilin tada hankali yana nan dawowa, amma yana bukatar karin hutu.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: