Tashin hankali yayinda kudin man jirgi ya tashi N265
Kudin man jirgin sama ta tashn N265 ga lita a Najeriya. Wannan na faruwa ne duk da cewa farashin kudi mai ya sauka a kasuwan duniya.
Wannan abu ya tayar da hankalin ma’aikatan jiragen sama kuma suna sa ran cewa wannan abu zai iya jan kulle filayen jirgin sama.
A Kano, Kaduna da wasu jihohin arewa, kudin man ya haura tsakanin N255 da N265. A legas kuma, anan sayarwa N240 zuwa N250, dangane da yawan man da mutum ke bukatan saya.
KU KARANTA: Yan PDP sunce Ali Modu Sherrif munafiki ne
Kimanin makonni 2 da suka gabata, kudin man ta a N220 a Legas, da kuma N230 a sauran wurare.
Tsakanin Junairu da Fabrairun 2016, kudin man na N120, amma cikin watanni 12, kudin ta ninka kanta.
Wani dan kasuwan mai ya tabbatar sa wannan tashin farashin ga jaridar Sahara Reporters. Majiyar ta dauran laifin wannan abu ga rattan da ke tsakanin Naira da dalar Amurka, wanda ya tashi daga N490 zuwa N506.
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng