Wani yayi wa uwar sa ciki kuma zai aure ta

Wani yayi wa uwar sa ciki kuma zai aure ta

– Wani Saurayi zai auri uwar da ta haife sa

– Yanzu haka wannan Amaryar tana da juna biyu; ‘Da ko kani?

– Bisa dukkan alamu dai Duniya ta zo karshe

Wani yayi wa uwar sa ciki
Wani yayi wa uwar sa ciki

Bisa dukkanin alamu dai Duniyar nan ta zo karshe don kuwa mun samu wani labari da ba mu taba jin irin sa ba. A Kasar Zambia wani saurayi ne zai auri mahaifiyar sa.

Wannan abu dai ya faru ne a wani Gari a can Kasar Zambia inda wani matashi Farai Mbereko mai shekara 23 ke shirin ya auri uwar sa mai shekaru 40. Kai kafin nan ma dai wannan yaro yayi wa Mahaifiyar ta sa ciki.

KU KARANTA: Ta kashe jaririn da ta haifa

Wani yayi wa uwar sa ciki kuma zai aure ta
Wani yayi wa uwar sa ciki kuma zai aure ta

Miss Mbereko mai dauke da juna biyu na wata 6 dai yanzu sun tsere da ita da Mijin na ta ko a ce ‘dan ta zuwa wani wuri inda ba a sani ba. Miss Mbereko dai ta rasa Mijin ta ne kwanakin baya, ta kuma zabi ta auri ‘dan ta saboda soyayyar da ta shiga tsakanin su, ‘yan uwan Mijin wannan mata dai da dama suna nema su aure ta, tace sam ga ‘dan cikin ta!

Wannan mata dai tace ita tayi hidima ga ’dan na ta don haka ita ta fi kowa cancanta ta auri kayan ta, ba wata mace ba. Wannan yaro dai ya bayyana cewa shi ne uban ‘dan uwar sa saboda kar ayi wa mahaifyar sa kallon banza, a dauka a waje tayi ciki. Nathan Mputirwa Dakacin wannan Gari dai yace ba su taba jin irin wannan haukan ba.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: