Karanta yadda wani matashi ya tsere daga hannun masu satar mutane

Karanta yadda wani matashi ya tsere daga hannun masu satar mutane

-Jam'in tsaro na civil defense ta samu nasarar ceto wani matashi daga hannun masu satar mutane a Maiduguri.

-Matashin da ya auna arziki ya ce, ya shiga wata moyar haya ne a inda aka barbada masa wata hoda da ta gusar masa da hankali.

Karanta yadda wani matashi ya tsere daga hannun masu satar mutane
Karanta yadda wani matashi ya tsere daga hannun masu satar mutane

Rudunar tsaro ta Civil Defence a ranar Lahadi 21 ga watan Fabarairu shekarar 2017 ta ce, jami'an ta sun samu nasarar ceto wani matashi mai suna Abdulkarim Garba daga hannun wasu da ake zaton masu satar mutane a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Babban kwamandan rundunar Ibrahim Abdullahi ne ya fadi haka a Maiduguri a wata hira da ya yi da wakilin Kamfanin dillancin labarai na Najeiya NAN.

Kwamandan ya ce, masu satar mutanen sun sace matashi Garba ne sun kuma yar da shi a unguwar Njimtilo da misalin karfe 5:00 na yamma a ranar Asabar.

Su kuma jami'an rundunar suna yawon sintiri a wannan unguwa sai suka cikaro da shi a cikin wani irin yanayi da ya sa suka soma bincikarsa.

Binciken nasu ya nuna cewa, matashin sunansa Abdulkarim Garba dan shekara 15, dan asalin jihar Yobe ne, kuma yana karatu ne makarantar koyon addinin Islama ta El Kanemi.

Shugaban rundunar ya kuma ce, a lokacin da jami'ansa suka gan shi, ba ya cikin hayyacinsa bai kuma san inda ya ke ba, bai kuma san inda za shi ba.

Sai dai daga baya ne ya yi bayanin cewa, "abin da zai iya tunawa shi ne ya shiga wata motar haya a mahadar kamfanin Borno Express".

"Amma sai ya tsinci kan shi a Njimtilo cikin mamaki, abin da zai iya tunanawa kawai shi ne a cikin motar ce wani ya barbada masa wata farar hoda wanda hakan ya sa ya rasa hankalinsa".

Garba wanda ya auna arziki ya ce, "da alama wadanda suka sace shi sun fahimci ba za su iya wuce shingen binciken ababben hawa na Njimtilo ba sai suka sauke shi suka kuma gudu"

A cewar shugaban rundunar, "daga bayanan da ya yi mana mun fuskanci cewa, Garba ya fada hannun masu satar mutane ne alamun niyyar yin tsafida shi, Allah kuma Ya kubutar da shi".

Shugaban rundunar Abdullahi Ibrahim ya yi kira ga jama'a da su rika kiyaye irin motoci da kuma babur masu kafa uku haya da suke shiga.

Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu

Aiko da naku ra'ayin dangane da wannan labari zuwa http://www.facebook.com/naijcomhausa ko kuma a http://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel