Mutumin da aka kama a gado da matar dansa yayi ikirarin cewa yayi ne don kudi
An kama wani mutumi, Jonathan Mutoro ido-da-ido yana lalata da matar dansa a kan gado.
Wani boka ne ya yaudari mutumin inda ya bukace shi da ya kwanta da matar dansa idan yana son yayi kudi.
Mutoro wanda ya fito daga kauyen Maravanyika a kasar Zimbabwe na cikin yaki da dansa a yanzu, John Mutoro wanda ya kama shi da hannunsa kan gado tare da matar sa, Easter Shoko.
An kai rahoton al’amarin ga kotun kauyen a take. Wani shugaba daga kotun mai suna, Chiyera, ya tabbatar da al’amarin ya kuma bayanna cewa yar Mutoro ce ta kama sa a yayinda yake cikin aikata abun.
KU KARANTA KUMA: ‘Yata da mijina suna da wata alaka, kuma bazan iya dakatar da shi ba – wata mata ta koka
Yace: “Yar Mutoro ce ta kama Mutoro da Shoko yayinda yake jima’i. yarinyar kuma ta fada wa yayanta wanda shine mijin Shoko kuma sun kai karan al’amarin kotun kauyen.”
Ya ci gaba da cewa Mutoro yayi ikirarin cewa wani boka ne ya fada mai ya aikata hakan saboda yayi kudi. Yace: “Ya yarda cewar ya aikata laifin kuma y aba dan nasa da matarsa hakuri. Ya tona asirin cewa wani boka ne ya ce mai ya kwanta da matar dansa idan yana so yayi kudi cikin dan kankanin lokaci.”
A cewar Cif din, Shoko bazata iya kin amincewa da sirikin ta ba saboda anyi mata alkawarin arziki. “Bazata iya kin amincewa da sirikin nata ba da ya bukaci Tarawa da ita tunda yayi mata alkawarin bata kaso a cikin dukiyar idan ya samu.”
Chiyere ya bukaci su biyun da suka aikata mummunan laifin da su biya kauyen shanaye uku.
Abun al’ajabi baya karewa!
Asali: Legit.ng