Ina raye! Shugaban kasa Buhari ya saki hujjar cewa yana nan da ransa

Ina raye! Shugaban kasa Buhari ya saki hujjar cewa yana nan da ransa

Bayan rahotanni zargin mutuwarsa a birnin UK, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da kuma samar da hujjar cewa yana raye kuma cikin koshin lafiya.

Ina raye! Shugaban kasa Buhari ya saki hujjar cewa yana nan da ransa
Ina raye! Shugaban kasa Buhari ya saki hujjar cewa yana nan da ransa

Shugaban kasar yaje shafinsa na Twitter ya saki wani hotonsa yana shakatawa a birnin UK yana kuma kallon shirin siyasa ‘Sunday Politics’ a Channels.

KU KARANTA KUMA: Dubi hotuna 10 na shugaban kasa Buhari da baku taba gani ba (hotuna)

An saki hoton ne dai-dai lokacin da ake haska shirin a Najeriya.

Babban dan adawan shugaban kasar gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose na cikin shirin a daren jiya inda yake zargin cewa yan matan Chibok da aka sace ya kasance shiri.

Ku tuna cewa fadar shugaban kasa ta karyata rahoton da wasu kafofin watsa labara sukayi na cewa shugaban kasa Buhari, wanda ke hutu a kasar waje ya mutu.

Zuwa yanzu dai an tabbatar da cewa rahoton karya ne shugaban kasa na nan da ransa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel