Jihar Katsina: Barayin shanu sun tuba, sun ajiye makamai

Jihar Katsina: Barayin shanu sun tuba, sun ajiye makamai

– Gwamnatin jihar Katsina ta bada lamuni ga barayin dabbobi

– Tsofaffin barayin shanun da dama sun mika wuya, sun ajiye makamai

– An samu maido bindigogi da dabbobi da dama

Jihar Katsina: Barayin shanu sun tuba, sun ajiye makamai
Jihar Katsina: Barayin shanu sun tuba, sun ajiye makamai

Gwamnatin jihar Katsina ta bada lamuni ga barayin dabbobi a Yankin. Hakan ta sa da dama sun ajiye makaman su ga hukuma. An dai samu bindigogi fiye da 300 da kuma dabbobi masu yawan gaske.

Bayanai sun nuna cewa an samu maido dabbobi sama da 28,000 da aka sata a baya. An dai kuma samu bindogin AK har guda 97 da kuma sauran kananan bindigogi fiye da 200. Daruruwan mutane ne dai suka mika wuya suka ajiye makaman na su yayin da Gwamnati ta bada lamuni.

KU KARANTA: Ka ji abin da asu neman Biyafara suka yi?

Sakataren Gwamnatin, Dr. Mustafa Inuwa ya bayyana haka a Garin Kankara idan aka mika makaman. Wannan dai yana cikin kokarin Gwamnatin na kawo karshen rikicin makiyaya da manoma. Tuni dai an mika mafi yawan dabbobin da aka maido ga masu su.

A Kaduna kuma, Dan Majalisar da ke wakiltar Karamar Hukumar Kaura da ke cikin Kudancin Jihar, Honarabul Gideon Gwani ya koka da yadda lamarin tsaro ya tabarbare a Yankin. Dan Majalisar yace Mutanen suna cikin matsala dare da rana.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng