Zahra Buhari tayi murnar cikarta wata daya da aure
Lokaci na gudu kuma wata daya bayan bikin Zahra Buhari da Ahmed Indimi, sarauniyar ta buga wani hoto don murnar cikarta wata daya da aure
Zahra Buhari a yanzu matar, yar shugaban kasar Najeriya mai ci a yanzu ta auri masoyinta, dan biloniyan Maiduguri Ahmed Indimi cikin biki mai kayatarwa a shekarar da ya gabata.
Auren wanda ya ja hankulan mutanen da dama, tare da wasu dake mata fatan samun dukkan farin ciki dake cikin aure.
KU KARANTA KUMA: Hadaddun hotunan yan matan Indimi a gurin bikin Mustapha Indimi
A bayyane yake cewa matashiyar bafulatanar ta cikin farin ciki kamar yadda aka ganta tare da mijinta suna yawon shakatawa a kyawawan kasashe, wanda ya hada da kasa mai tsarki inda suka fara yada zango bayan aurensu.
Bayan wata daya, ta buga wani rubutu a shafin zumunta, tare da wani sabon suna ZMBI (Zahra Muhammadu Buhari Indimi). Cikin murta tayi bikin cikarta wata daya a sabon aurenta. Kalli kasa:
KU KARANTA KUMA: Wata mata ta saka hoton ta cikin hotunan auran Zahra Buhari
Asali: Legit.ng