Sevilla ta karya alkarin Real Madrid
An kawo karshen buga wasanni 40 a jere da Real Madrid ta yi ba tare da an doke ta ba a wasanni, bayan da Sevilla ta ci ta 2-1 a wasan La Liga da suka yi a ranar Lahadi.
Cristiano Ronaldo ne ya fara ci wa Madrid kwallo a bugun fenariti, bayan da mai tsaron ragar Sevilla Sergio Rico ya yi wa Dani Carvahal keta.
Daga bisani Sergio Ramos ya ci gida wanda hakan ya sa wasa ya koma 1-1 kafin Stevan Jovetic ya zura ta biyu.
Rabon da a doke Real Madrid a wasa tun cikin watan Afirilun bara.
Sai dai duk da cewa tana mataki na daya a kan teburin La Liga, yanzu saura maki daya ya rage tsakaninta da Sevilla ta biyu.
Real Madrid tana da kwantan wasa daya a gasar cin kofin La Liga, kuma Barcelona ta koma ta uku a kan teburin gasar bana.
Asali: Legit.ng