Ba ruwan mu da rikicin Kaduna inji fulani

Ba ruwan mu da rikicin Kaduna inji fulani

A jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, kungiyar Fulani ta musanta zarge-zargen da wasu ke yi cewa su ne ke kai hare-hare a kudancin jahar.

Ba ruwan mu da rikicin Kaduna inji fulani
Ba ruwan mu da rikicin Kaduna inji fulani

A wani taron manema labarai a Kaduna, al'ummar Fulanin sun ce ba zaunannun Fulani na kudancin jihar ne ke kaddamar da hare hare ba, mai yiwuwa wasu Fulani ne dake zuwa yankin daga waje.

KU KARANTA KUMA: Kyakkyawan sauyi na nan tafi a 2017 inji Shugaba Buhari

A halin yanzu dai an kafa dokar hana fita ta sa'o'i 24 a wasu kananan hukumomi na jihar sanadiyyar rikice-rikice tsakanin fulanin da wasu kabilu.

Rahotanni sun ce an yi asarar rayuka da dukiyoyi a hare hare na baya bayan nan da wasu 'yan bindiga suka kaddamar a Kudancin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel