Sojin ruwan Najeriya sun yi abin kwarai

Sojin ruwan Najeriya sun yi abin kwarai

– Sojojin ruwa na Najeriya sun takawa tsageru burki a Jihar Ribas

– Sojojin Kasar sun yi nasarar karbe mai daga hannun Tsagerun

– Ana ta fama da Tsageru a Yankin na Ribas da sauran Kudancin Kasar

Sojin ruwan Najeriya sun yi abin kwarai
Sojin ruwan Najeriya sun yi abin kwarai

Sojin Najeriya na ruwa sun taka rawar gani inda suka gano wasu wuraren aikin mai da Gwamnati ba ta san da su ba a Yankin Jihar Ribas. Wata Bataliyar Sojojin ruwa na Kasar ne tayi wannan gagarumin aiki Inji Jaridar Premium Times.

Jaridar tace Sojojin sun dura wani wuri da ake aikin tace man Kasar a boye a wani Yanki da ake kira Taraba a Jihar Ribas din. Sojojin sun samu nasarar karbe wasu manyan duro na mai da ya fi lita 70, 000. An samu wani man ma gurbace da ruwa a hannun Tsagerun.

KU KARANTA: An damke Babban Dan ta'addan Duniya

Wannan dai yana cikin kokarin da Sojin Kasar suke yin a kokarin an tsaida barna a Yankin Kasar mai arzikin mai. Sojojin dai sun samu nasarar cafke Tsagerun kaf. An dais aba fafatawa tsakanin Tsagerun da Rundunar Operation Delta Safe na Sojin Kasar.

Da hutun Kirismetin nan ne Shugaban Kasar, Muhammadu Buhari ya nemi a roki Jama’an Neja-Delta, da kuma Tsagerun Yankin masu barna, da su zauna a sasanta. Shugaban Kasar yace babu dalilin barnatar da arzikin Kasar

Asali: Legit.ng

Online view pixel