Kyakkyawan bikin Halima Buhari a 2012
Gagarumin bikin Zahra Buhari ya yi fice a yanar gizo da fadin birnin tarayya Abuja kuma yadda aka gudanar da bikin zai s aka tunanin ko ita kadai ce yar shugaban kasa.
Kamar yadda kuka sani, Halima Buhari ta kasance daya daga cikin yayan shugaban kasa Buhari. Abun kyan shine ta kasance ya ta farko ga uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari kuma kwanan nan ta kammala makarantar shari’a. Ba kamar Zahra wacce ta shiga dakin aure kwaanan nan, Halima tayi aure tun shekarar 2012. Auren nata ya kasance kayattace kamar na kanwar ta.
Halima wacce ta kasance uwa a yanzu ta yi aure da Babagana Sheriff biki mai kyau kafin mahaifinta ya zama shugaban kasa. Kalli bidiyo a kasa:
KU KARANTA KUMA: Yar sarkin Kano, Siddika Sanusi ta saki hotunan bikin wankan amarya
Asali: Legit.ng