LABARI DA DUMI-DUMI: An sanya dokar hana fita a Kafanchan jihar Kaduna

LABARI DA DUMI-DUMI: An sanya dokar hana fita a Kafanchan jihar Kaduna

Shugaban karamar hukumar Jema’a na jihar Kaduna, Dr. Bege Katuka ya sanya dokar hana fita na sa’oi 24 a garin Kafanchan samamakon babban zanga-zanga da akeyi kan ci gaba da kashe-kashe da akeyi a Kudancin Kaduna.

LABARI DA DUMI-DUMI: An sanya dokar hana fita a Kafanchan jihar Kaduna
LABARI DA DUMI-DUMI: An sanya dokar hana fita a Kafanchan jihar Kaduna

Kafanchan ya kasance hedkwatan karamar hukumar Jema’a haka kuma cibiyar ciniki na yankin kudancin Kaduna.

A safiyar yau daruruwan matasa, mata da yara sun shiga unguwa don yin zanga-zanga kan kisan kiyashi da yan bindida wadanda ake zargin makiyaya ne sukayi ma masoyansu.

KU KARANTA KUMA: Rikicin tattalin arziki: Dole Najeriya ta ranto $30billion - Gbajabiamila

A cewar ciyaman din an sanya dokar hana fitan ne domin guje ma tashin fitina da taka doka a yankin.

Cikakken bayani na nan zuwa…

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: