Dambarwar siyasar jihar Ribas: Akwai yiwuwar PDP taji kunya
Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan rikicin zaben jihar Rivers da ke kudancin kasar.
Kwamitin wanda ya kunshi kwararrun jami’an tsaro, zai zurfafaf bincike kan wani sakon murya da ake zargi ta Gwamna jihar ne Nyesom Wike, in aka ji yana yin bazarazar kashe jami’an hukumar zaben kasar, matukar suka gaza taimaka wa jam’iyyarsa ta PDP samun nasara a zaben na ‘yan majalisu.
An dai ji muryar na yin barazanar kisa ko kuma a dawo da cin hancin da aka bai wa jami’an INEC da ba a fadi sunayensu ba.
Sai dai ofishin gwamnan ya musanta zargin, yayin da ake sa ran fitar da sakamakon binciken nan da kwanaki 30, don bayyana shi ga jama'a.
Asali: Legit.ng