Hukumar JAMB za ta rage makin shiga Jami’a
- Hukumar JAMB mai gudanar da jarrabawar shiga makarantu na gaba da sakandare za ta rage makin da ta sa
- Shugaban Hukumar JAMB din yace wasu Jami’o’i na samun wahalar aiki da wannan tsari
- JAMB din za ta kawo wani tsari domin ganin na gaba da Sakandare sun samu shiga Jami’o’i
Da alamu dai cewa Hukumar JAMB mai gudanar da jarrabawar shiga makarantu na gaba da Sakandare a Kasar za ta rage makin da ta saka a baya na samun shiga Jami’o’in Kasar. Shugaban Hukumar Jarrabwar, Farfesa Ishaq Oloyede yayi wannan magana ne a wajen wani taro da aka gudanar game da shiga Makarantun gaba-da-Sakandare.
Jaridar The Nation tace, Farfesa Ishaq Oloyede, Shugaban Hukumar JAMB din yace an dauki mataki kayyade maki 180 a matsayin makin da ake bukata na shiga Jami’o’in Kasar a wani taro da aka yi a baya. Sai dai yanzu Jami’o’i da dama kuma sun nuna cewa ba za su iya aiki da wannan tsari ba.
KU KARANTA: Darajar Naira ta tashi
Wasu Jami’o’i, musamman maus tasowa, idan suka ce sai wanda ya samu maki 180 zai shiga Jami’ar, to ba za su dauki kowa a Makarantar ba. Sai dai kuma a wani bangare da daman a kukan cewa sun samu fiye da maki 180 da ake nema, amma sun gaza samun shiga Makarantun na gaba da Sakandare.
Wannan shekarar ne Gwamnatin Tarayya ta dai kashe tsarin Jarrabawar Post-UTME domin marasa karfi su samu shiga Jami’a domin daukar karatu.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
https://youtu.be/wXmmTEAKDxo
Asali: Legit.ng