Mutane 6 da suke rike da madafan iko a Najeriya

Mutane 6 da suke rike da madafan iko a Najeriya

- Ana ta kukan cewa wasu mutane sun rike madafan iko a gwamnatin Baba Buhari

- Ko su wanene wadannan mutane da ba a san su ba?

- Kwanaki dai har sai dai matar shugaban kasa, Aisha Buhari ta koka a BBC

Mutane 6 da suke rike da madafan iko a Najeriya

 

 

 

 

Kwanakin baya, matar shugaban kasa, Aisha Buhari ta koka da yadda wasu mutane da ba ayi yakin zabe da su ba suka rike madafan iko a Gwamnatin mai gidan ta a Gidan BBC. Haka ma Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya taba cewa wasu sun karbe madafan iko daga hannun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Ko su waye wadannan mutane? Legit.ng sun cinko mutane 6 da ake zargin su su ke rike madafan iko a Kasar a halin yanzu.

KU KARANTA: Mutanen Jonthan sun goyawa Shugaba Buhari baya

MAMMAN DAURA

Mamman Daura ya zama tamkar Mataimakin Shugaban Kasa, ko da bai da wani takamamen Ofishi, yana cikin wadanda suke rike da madafan iko a Kasar. Ko a lokacin da Buhari yayi mulkin Soja, da shi aka dama. Shugaba Buhari kawu yake a wurin sa, duk da Mamman ne babba.

ABBA KYARI

Shugaban ma’aikatan Gidan Gwamnati, Abba Kyari. Kyari tsohon Janar ne na Soja, kuma danuwan Shugaba Buhari ne. Tun zamanin Gawon ake damawa da shi.

BABACHIR DAVID LAWAL

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir yana daya daga cikin wadanda suke rike da madafan iko a Kasar nan, kuma ba ya shakkan hakan. Shugaba Buhari na jin ta bakin sa.

[A saurari na kashi biyu]

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng