Olympics: Najeriya ta Kuma Kwaba Abin Kunya a Idanun Duniya a Mulkin Tinubu
- Yar Najeriya da ke gasar tseren a kasar Faris a cikin rukunin wasannin Olympics ta bayyana halin da ta shiga yayin da ta rasa keke
- Ese Ekpeseraye ce ke wakiltar Najeriya a gasar tseren keke na duniya a 2024 da a yanzu haka ke gudana a kasar Faris
- Ministan wasanni na kasa, John Enoh ya bayyana makudan kudin da gwamnatin Najeriya ta ware ga wasannin Olympics na bana
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Yar wasan tseren keken Najeriya a gasar Olympics ta rasa keken hawa yayin gasar a kasar Faris.
Ese Ekpeseraye ta bayyana dalilin da yasa aka taimaka mata da aron keke domin samu ta shiga gasar.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa gwamnatin Najeriya ta ware kudi har Naira biliyan 12 domin wasannin Olympics na shekarar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Najeriya ta yi abin kunya a Olympics
Ese Ekpeseraye ta bayyana cewa an kirata ta yi tseren keke a Olympics amma a lokacin ba ta da keke da za ta yi amfani da ita.
Hakan ya sa yan gasar Olympics daga kasar Jamus suka ba ta taron keke da ta yi amfani da shi domin shiga tseren.
Dalilin rashin samun keken Olympics
Punch ta wallafa cewa Ese Ekpeseraye ta bayyana ba ta damar shiga tseren a kankanin lokaci a matsayin dalilin rashin samun keken.
Wannan shi ne karon farko da wani dan Najeriya ya shiga gasar Olympics ya rasa keke, sai dai wasu na ganin ba laifin mahukuntar kasar ba.
Kudin da Najeriya ta warewa Olympics
Ministan wasanni a Najeriya, John Enoh ya tabbatar da cewa Najeriya ta ware kudi Naira biliyan 12 domin wasannin Olympics na bana.
Bayan kudin da gwamnati ta ware majalisar wakilai ta amince da ware Naira miliyan 100 ga yan wasan Najeriya da ke Olympics.
Najeriya ta samu tasgaro a Olympics
A wani rahoton, kun ji cewa an dakatar da ‘yar wasan damben Najeriya, Cynthia Ogunsemilore daga gasar Olympics bayan gwaji ya nuna tana ta'ammali da kwaya.
Hukumar ITA ta ce gwajin jinin da aka yiwa Cynthia ya nuna cewa tana tu'ammali da kwayar furosemide wadda ke kara kuzari a jiki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng