Kungiyar Kwallon Manchester United Ta Raba Jiha Da Cristiano Ronaldo

Kungiyar Kwallon Manchester United Ta Raba Jiha Da Cristiano Ronaldo

  • Zama Doya da Manja dake tsakanin Erik Ten Hag da Cristiano ya zo karshe, an yi baran-baran
  • Kungiyar Manchester United ta aba jiha da daya daga cikin manyan yan kwallo a tarihinta
  • Ronaldo ya balla teburin alakan dake tsakaninsa da kungiyar Manchester a hirarsa da Piers Morgan

Kungiyar Kwallon kafa ta Manchester United mai taka leda a Ingila ta sanar da cewa ta yi hannun riga da shahrarren dan kwallo, Cristiano Ronaldo.

Manchester a ranar Talata cewa Ronaldo ya kwashe kayansa ya bar mata kungiya bayan yarjejeniyar raba jiha da sukayi.

A jawabin da Manchester ta fitar a shafinta na yanar gizo, tace:

"Cristiano Ronaldo zai bar Manchester United bayan yarjejeniya, cikin gaggawa."
"Kungiyar na gode masa bisa gudunmuwar da ya bada bayan taka mata leda har sau yi a Old Trafford."

Kara karanta wannan

Uban 'Yan Sa'a: Wani Mutumi Ya Taki Sa’a, Ya Ci Naira Tiriliyan 1 a Wajen Caca

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ronaldo Ya yi Kaca-kaca da Man Utd, Yace Bai Ganin Girman Kocin Kungiyar

A wata hira da ya yi da Piers Morgan, ‘dan wasan gaban Manchester United, Cristiano Ronaldo ya yi bayanin halin da ya tsinci kan shi.

A hirar da Piers Morgan ya yi da Cristiano Ronaldo a shirinsa na TalkTV, a nan aka ji ya soki kungiyar da yake bugawa wasa.

Ronaldo ya yi ikirarin abubuwa ba su tafiya daidai a kulob din tun da Sir Alex Ferguson ya ajiye aiki a 2013, ya kuma ce bai ganin girman Eric Ten Haag.

Skysports ta rahoto ‘Dan wasan mai shekara 37 a Duniya yana cewa kocin kungiyar watau Erik ten Hag bai ganin darajarsa, don haka shi ma bai girmama sa.

Cristiano Ronaldo ya Dauke ‘Ya ‘yansa daga Ingila, Man Utd ta Maida Masa Martani

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida