Kai tsaye: AFCON: An tashi Najeriya ta bizne Guinea Bissau 2-0
Yan kwallon Najeriya Super Eagles suna fara buga wasarsu na uku a gasar kofin nahiyar Afrika tare da yan kwallon kasar Guinea Bissau.
Ana buga wannan wasa ne a filin wasan Roume Adjia dake garin Garoua, kasar Kamaru misalin karfe 8 na yamma.
Najeriya ta lallasa kasar Masar da Sudan a wasarta ta farko da na biyu.
Ga jerin yan wasan da aka zaba yau:
An baiwa Najeriya kwallon, Najeriya ta ci kwallo ta biyu
Alkalin wasa ya canza ra'ayinsa bayan na'urar VAR ta sake duba kwallon
Najeriya ta sake canji biyu
Kelechi Nwakali ya fita, Franka Onyeka
Ebuehi ya fita, Olisah Ndah ya shiga
Najeriya ta ci kwallo ta biyu amma alkalin wasa yace offside
Najeriya ta ci kwallo ta biyu amma alkalin wasa yace offside
Bayan cin kwallo, an cire Sadiq Musa da Ejuke
Najeriya ta yi sauyin yan wasanni biyu.
Sadiq Musa ya fita, Peter Olayinka ya shiga
Ejuke ya fita, Moses Simon ya shiga
Sadiq Umar ya zurawa Guinea Bissau kwallo
Dan wasan Najeriya, Sadiq Umar, ya zura kwallo ta farko ragar Guinea bissau daidai minti
An tafi hutun rabin lokaci
An tafi hutun rabin lokaci kuma babu ci har yanzu tsakanin Najeriya da Guinea Bissau
Saura kiris Sadiq Umar ya ciwa Najeriya
Saura kiris Dan kwallon Najeriya, Sadiq Umar, ya zura kwallo ta farko.
Sadiq har ya yanke mai tsaron ragar Guinea Bissau amma yan masu jajayen kaya sun yi masa yawa.