AFCON: Kowane ‘Dan wasan Super Eagles zai tashi da $10000 bayan doke Sudan da Masar
- Za a rika biyan ‘Yan tawagar Super Eagles fam $5000 da zarar sun yi nasara a wasa a gasar AFCON
- Kowani dan dan kwallon kasar Najeriya yanzu ya samu $10000 bayan doke kasashen Masar da Sudan
- An yi yarjejeniya NFF za ta dunkule wadannan kudin a biya taurarin idan an kai mataki na gaba
Cameroon - ‘Yan wasan kungiyar Super Eagles na Najeriya za su karbi $10,000 a dalilin nasarar da suka samu a wasanni biyu a gasar kofin nahiyar Afrika.
Jaridar Punch ta ce ‘yan wasan Najeriya za su samu wannan kudi ne bayan sun doke kasashen Masar da kuma Sudan a wasan rukuni da aka buga a yanzu.
Hukumar kula da kwallon kafan Najeriya, NFF ta cin ma matsaya da ‘yan wasan a kan yadda za a rika biyan kudi idan sun yi nasara ko an tashi kunnen-doki.
Rahoto ya bayyana cewa an yi wannan zama tsakanin jami’an NFF da ‘yan wasan ne a garin Garuoa, kasar Kamaru, kafin a fara wasannin gasan cin kofin.
Nawa za a rika biyan 'Yan wasa?
Bayan kowace nasara da aka samu, duk wani ‘dan wasan Super Eagles zai tashi da fam $5000. Idan an yi kunnen-doki, za a ba kowane ‘dan rabin kudin, $2500.
Wata majiya a NFF ta shaidawa jaridar cewa haka aka yi yarjejeniya za a biya bayan kowane wasa. Idan ba a samu nasara ba, ‘yan wasan ba za su samu komai ba.
Za a fitar da wadannan kudi a dunkule bayan Najeriya tayi nasarar kai wa zuwa mataki na gaba. Akwai yiwuwar kudin su karu idan Eagles tayi nasara a wasan karshe.
Najeriya tana ta abin yabo
Kawo yanzu Super Eagles tana cigaba da kokari a gasar ta AFCON inda tayi nasarar doke Masar da ci 1-0 a wasan farko, sannan ta doke kasar Sudan da ci 3-1.
Nasarar da Super Eagles ta samu a kan kasar Sudan a filin wasan Stade Roumdé Adjia ya yi sanadiyyar da Najeriya ta samu kai wa zuwa mataki na gaba a gasar.
Kwallayen Samuel Chukwueze, Taiwo Awoniyi da Moses Simon suka kai Eagles zuwa zagaye na gaba.
...Duk da an rasa Victor Osimhen
Kafin a fara gasar wannan shekara ne aka ji cewa an yi gwaji an tabbatar da cewa tauraron Super Eagles, Victor Osimhen ya na dauke da kwayar cutar COVID-19.
Kungiyar Napoli ta bada sanarwa cewa Coronavirus ta harbi ‘Dan wasan gaban na Super Eagles wanda aka sa ran shi ne zai jagoranci gaban Najeriya a Kamaru.
Asali: Legit.ng