Kotu ta samu ‘Dan wasan Real Madrid, Karim Benzema da laifi, an yanke masa dauri a gidan yari

Kotu ta samu ‘Dan wasan Real Madrid, Karim Benzema da laifi, an yanke masa dauri a gidan yari

  • An samu ɗan wasan Real Madrid, Karim Benzema da laifin cin amanar wani tsohon abokin wasansa
  • Karim Benzema ya je kotu ne a kan batun da ya shafi wani faifan bidiyon lalata na Mathieu Valbuena
  • Wannan badakala ta sa tsohon ɗan wasan na Lyon ya yi shekaru bai bugawa kasarsa ta Faransa ba

Rahotanni daga BBC sun tabbatar mana da cewa Alkali ya kama ɗan wasan gaban kungiyar Real Madrid da ke kasar Sifen, Karim Benzema da laifin cin amana.

BBC tace kotu ta samu ɗan kwallon kafan ne da laifin da ake tuhumarsa da shi na cin amanar wani tsohon abokin wasansa a kasar Faransa, Mathieu Valbuena.

A sakamakon haka, Alkali ya yankewa Karim Benzema hukuncin ɗaurin shekara daya a gidan yari.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya yi martani kan fastocinsa dake yawo na takarar shugaban kasa a 2023

Goal.com ta ce baya ga ɗauri, kotu ta umarci ɗan kwallon ya biya tarar €75,000 a dalilin rawar da ya taka a badakalar fai-fen bidiyon lalatar Mathieu Valbuena.

Benzema ya tsaya a kotu a watan jiya ne bisa zarginsa da ake yi na yaudarar tsohon ‘dan wasan Lyon, Valbuena a kan wani bidiyon lalata da ake zargin ya fito.

'Dan wasan Real Madrid
Karim Benzema yana bugawa kasar Faransa
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Benzema zai daukaka kara?

Wannan abu ya faru sama da shekaru biyar kenan da su ka wuce. Da aka tuntubi lauyoyin Benzema, sun tabbatar da cewa za su nemi su daukaka karar.

“Lamarin hukuncin shari’ar nan ya ba mu mamaki. Akwai bukatar mu daukaka kara. Za a wanke shi idan aka daukaka karar.” – Wani lauyan Benzema.

‘Yan damfara sun yi barazanar sakin wani bidiyon lalata da Mathieu Valbuena ya fito a ciki idan har bai biya makudan kudi ba, ana zargin da hannun Benzema a nan.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi a jihar Nasarawa kan kisan wasu makiyaya

Baya ga tarar N34m, Benzema, ya na iya shafe shekaru biyar a gidan yari. Tauraron bai halarci zaman kotu ba, kuma babu tabbacin cewa za a tsare a gidan kaso.

Messi ya yi magana a kan Ronaldo

Kwanan nan aka ji Lionel Messi ya na yabawa halin Cristiano Ronaldo bayan komawarsa kungiyar Manchester United daga kungiyar Juventus a shekarar nan.

Babban ‘Dan wasan yace tsohon ‘dan wasan na Real Madrid bai sha wahalar sabawa da Ingila ba, ganin yadda ya cigaba da zura kwallaye a raga kamar yadda ya saba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng