Ronaldinho da shahararrun ‘Yan wasan kwallon kafa 6 da suka tsiyace bayan sun yi ritaya

Ronaldinho da shahararrun ‘Yan wasan kwallon kafa 6 da suka tsiyace bayan sun yi ritaya

Wasan kwallon kafa yana kawo kudi mai yawan gaske. Baya ga shahara da suna da ‘dan wasa zai yi

Sai dai kuma babu tabbacin za a mutu a haka, ‘yan wasa da-dama sun tsiyace da suka daina buga kwallo

Duk da irin makudan kudin da wadannan shahararrun taurari su ka tara, yanzu ba su da komai a rayuwa

Legit.ng Hausa ta tattaro wasu daga cikin tsofaffin ‘yan kwallon da yanzu rayuwarsu ta zama abin tausayi. A halin yanzu su na fama da muguwar fatara da kadaici.

1. Emmanuel Eboue

Na farko a jerin na mu shi ne tsohon ‘dan wasan kasar Ivory Coast, Emmanuel Eboue. Tsohon ‘dan wasan na Arsenal ya talauce bayan ya rabu da mai dakinsa.

2. Eric Djemba-Djemba

Kara karanta wannan

Da duminsa: ISWAP sun sake kai hari, suna luguden wuta a Borno da kone gidaje

Jaridar The Nation tace Eric Djemba-Djemba bai da komai a yau, duk da ‘dan wasan na Afrika ta Kudu ya yi kwallo da irinsu Cristiano Ronaldo a Manchester.

3. Royson Drenthe

Royson Drenthe yana cikin tsofaffin ‘yan wasan da yanzu suke ta kansu. Tsohon ‘dan wasan na Real Madrid ya fito da bakinsa kwanaki yana cewa ya yi asarar £3.3m.

4. Brad Friedel

Duk da an rika biyansa makudan kudi a Aston Villla, tsohon mai tsaron ragar kasar Amurka ya talauce bayan ya yi ritaya a sakamakon bashi da ya yi masa katutu.

Ronaldinho
Gaucho Ronaldinho Hoto: www.besoccer.com
Asali: UGC

5. John Arne Riise

John Arne Riise ya yi tashe da yake bugawa kungiyar Liverpool. Jim kadan da yin ritaya, sai aka ji ‘dan wasan bayan ya talauce, bayan ya fada wata badakala.

6. James

Ko da ya samu kusan Dala miliyan 30 da kwallon kafa, tsohon mai tsaron ragar Ingila, James ya dawo bai da komai. James ya tsiyace a 2014 da ya saki matarsa.

Kara karanta wannan

Harin ISWAP a Borno: Abubuwan da ya kamata ku sani game da Janar din aka kashe

7. Ronaldinho

Jaridar The Sun ta na sa Ronaldinho cikin ‘yan kwallon da suka tsiyace. Amma wasu na ganin cewa halin tauraron na kasar Brazil bai kai a ce ya tsiyace kar-kaf ba.

Labarin Faiq Bolkiah

A wani rahoto da mu ka fitar a yau, kun ji cewa ko da bai yi suna sosai a Duniya ba, da wuya a samu ‘dan kwallon da ya fi Faiq Bolkiah mai shekara 23 kudi a Duniya.

Ana tunanin Bolkiah ya mallaki sama da Dala biliyan 20, kimanin Naira tiriliyan 8 kenan. Wannan 'dan wasa ya samu wadannan makudan kudi ba ta kwallo ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng