Ana rade-radin PSG za ta kori Sergio Ramos tun kafin ya fara buga mata wasanni
- Kungiyar Paris Saint-Germain ta tanka masu rade-radin cewa tana ta neman kai da Sergio Ramos.
- Darektan wasannin na kungiyar PSG, Leonardo Araujo yace babu gaskiya a jita-jitar da ke yawo.
- Araujo yace tun farko PSG ta san halin da Sergio Ramos yake ciki kafin su dauko shi daga Madrid.
Paris - Kungiyar Paris Saint-Germain ta musanya rahotannin da suke yawo cewa tana tunanin katse kwantiragin Sergio Ramos, ta sallami ‘dan wasan nata.
Jaridar Football Espana ta karyata jita-jitar cewa PSG za ta raba gari da ‘dan wasanta, Sergio Ramos.
Har yanzu Sergio Ramos bai fara bugawa kungiyar kwallon kafan na kasar Faransa ba. A kakar shekarar nan ne PSG ta dauko ‘dan wasan daga birnin Madrid.
‘Dan wasan bai bugawa Real Madrid wasanni 30 a shekarar nan saboda yana fama da rauni. Amma duk da haka kungiyar PSG ta dauko ‘dan wasan a kyauta.
Watanni uku kenan da zuwan Sergio Ramos kasar Faransa, amma bai fara buga wasa ba. Rahotanni sun ce har yanzu ‘dan kwallon yana ta fama da rauni.
Hakan ya sa jaridar Le Parisien ta kawo rahoto cewa za a iya soke yarjrjeniyar Ramos da kungiyar PSG.
PSG ta yi magana ta bakin Leonardo Araujo
Darektan wasanni na kungiyar ta birnin Faris, Leonardo Araujo yace babu gaskiya a rahotannin da ake ji na cewa za su raba gari da sabon ‘dan wasan na su.
Leonardo Araujo yace sun san halin da ‘dan kwallon mai shekara 35 yake ciki kafin su mika masa kwantiragin shekaru biyu ya sa hannu a tsakiyar shekarar nan.
“Mun san Sergio Ramos yana da ciwo.” – Leonardo.
“’Yan jaridun kasar Sifen suna wasa da hankali ne, duk mun san yana da matsala. Mun san abin da yake faruwa a nan.”
Ramos ya zama abokin wasan Messi
Idan ba ku manta ba, Lionel Messi, Cristiano Ronaldo, da Sergio Ramos suna cikin yaurarin ‘Yan wasa da suka canza kulob a kakar shekarar nan ta 2021.
An ji cewa Sergio Ramos ya yi wa Lionel Messi tayin zama a gidansa kafin ya samu matsuguni a kasar Faransa. Bayan zuwan Ramos ne PSG ta dauko Messi.
Asali: Legit.ng