Jihar Zamfara
Bayan dawowa Majalisar Dattawa da aka sabunta a yau Talata 30 ga watan Afrilu, wasu sanatoci sun ba hammata iska kan yadda tsarin wurin zama ya ke.
Sarkin Kwatarkwashi a jihar Zamfara, Abubakar Ahmed Umar ya bayyana cewa 'yan ƙasashen ketare da kuma ma'adinai a Arewacin Najeriya ne silar matsaar tsaro.
A safiyar ranar Juma'a, 26 ga watan Afrilu 'yan bindiga suka kai hari kauyen Maradun da ke jihar Zamfara inda suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu 30.
Wasu 'yan bindiga sun kai farmaki fadar Sarkin Zurmi a jihar Zamfara inda suka hallaka mutane uku yayin da suka lalata karfunan sabis a yankin yayin farmakin.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, inda suka hallaka mutum uku da sace wasu.
Rahotanni daga jihar Zamfara sun nuna cewa wasu ƴan uwan amarya sun taru sun kashe ɗan bindiga ɗaya kuma sun kwato bindigu a titin Talatan Mafara zuwa Gusau.
Tsohon sanatan Zamfara ta Tsakiya, Sanata Kabiru Marafa, ya caccaki karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, kan sukar da ya yi wa Dattawan Arewa.
Al'ummar yankin Bini na karamar hukumar Maru sun yi gudun hijira zuwa gidan gwamnatin jihar Zamfara bayan janye dakarun sojoji daga yankinsu. sun nemi mafaka
An ruwaito cewa akalla fararen hula 3 ne suka mutu a wani hari da 'yan bindiga suka kai kauyen Tsafe da ke jihar Zamfara, yayin da suka yi artabu da sojoji.
Jihar Zamfara
Samu kari