Albashin ma'aikata
Kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki, ta tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki 7 a birnin tarayya, kan rashin biyan albashi, karancin ma'aikata da sauransu
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC), ta bayyana cewa mafi karancin albashin da ake biyan ma'aikata ya yi kadan. Ta bukaci gwamnati ta yi gaggawar sake duba shi.
Gwamnoni da dama sun haura dokar mafi karancin albashin Najeriya watau N70,000, jihar Imo ce a sahun gaba bayan Uzodinma ya yi kari zuwa N104,000.
Gwamnatin Abia ta sallami ma'aikata shida daga aiki bayan bincike ya gano yadda suka yi magudi a tsarin biyan albashi, suka rika karbar kudi fiye da hakkinsu a wata.
A labarin nan, za a ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana yadda ta ceto wadansu jihohi 27 na kasar nan daga matsalar gaza biyan albashin ma'aikata.
NLC ta yi kira ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu da ya ƙara mafi ƙarancin albashi daga N85,000 zuwa N150,000 ga ma'aikatan Legas, saboda karuwar tsadar rayuwa.
Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya haura mafi karancin albashin ma'aikata na kasa, ya amince da N90,000 ga karamin ma'aikaci a kowane wata.
Manyan jami'ai da mukaminsu ya fara daga mataimakin kwanturola, kwanturola, babban kwamanda zuwa sama, za su ci gaba da karbar albashi har zuwa lokacin mutuwarsu.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya fitar da sabon mafi karancin albashi ga malaman manyan makarantu, ma'aikatan lafiya da sauran ma'aikatan jihar.
Albashin ma'aikata
Samu kari