Albashin ma'aikata
Ma’aikatan NiMet sun fara yajin aiki a dukkanin fadin Najeriya. Ma'aikatan sun yi korafi na karancin albashi da yanayin aiki mai kyau. Sun nemi a dauki mataki.
Gwamnatin Kano ta biya N21bn daga cikin Naira biliyan 48.6 da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta hana wasu daga cikin 'yan fansho da suka hidimtawa jihar.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya tuna da ma'aikatan da suka yi ritaya da wadanda suka rasu. Gwamnan ya umarci a fitar da kudade domin biyansu hakkokinsu.
Kungiyoyin kwadago a Ribas sun yi barazanar tsunduma yajin aiki, inda suka bukaci Shugaba Tinubu da ya janye dokar ta-baci da ta hana a biya albashin ma’aikata.
Gwamnatin Kano ta bukaci ma’aikatan jihar da su tantance albashinsu na Maris, kafin ta fara biya, tana mai cewa za a biya kafin Sallah don su samu walwala.
ICPC ta gurfanar da jami’in NIS, Abubakar Aseku, bisa zargin karɓar N17.6m daga ma’aikatu uku. Kotu ta ba shi beli, an daga shari’a zuwa Afrilu 29.
Wasu daga cikin tsofaffin ma'aikatan da suka yi ritaya a jihar Kaduna, sun gudanar da zanga-zangar lumana. Sun bukaci Gwamna Uba Sani ya biyasu hakkokinsu.
Shugaban kamfanin MTN Najeriya, Karl Toriola ya shiga jerin manyan shugabannin kamfanoni da suka fi ɗibar albashi mai tsona a Najeriya, yana samun N850m.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da mukaddashin shugaban ma'aikatan jihar, Salisu Mustapha kan zargin cire kudi daga albashin ma'aikata ba bisa ka’ida ba.
Albashin ma'aikata
Samu kari