Aikin noma a Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta ce tsarin sauya fasalin takardun Naira da CBN ya aiwatar ya jefa manoma da yawa cikin fatara da talauci, ya jawo karancin wadatar abinci.
Wasu mata wadanda ke sana'ar sayar da rake sun bayyana damuwarsa kan karancin riba da rashin wadatar raken a bana. Manomin rake duk dai a Kadunan ya fadi dalili.
Gwamnatin Jigawa ta nemi Shugaba Bola Tinubu ya karasa aikin noman rani a yankin Hadejiya, an roki a gama aikin da aka fara lokacin Shagari a 1983.
Yan bindiga sun ajiye wa manoman Kontagora wasika a gonakinsu, inda suka bukaci kowanne manomi ya biya wa gonarsa harajin naira miliyan 30, ko kuma su konasu.
Idan manomi ya yi sa'a gonarsa ta yi kyau, sai ya biya kusan N100, 000 kafin ya yi girbi. ‘Yan bindiga na karba a hannun manoma kafin a cire kayan gona a Kaduna.
Kayan abinci sun yi tsada a dalilin rashin samun taki, rashin kyawun noman damina, rufe iyaka da kokarin gwamnati ya sa musamman shinkafa za ta fi karfin talaka.
Manoma sun shiga tsahin hankali a wasu ƙauyuka akalla 15 da ke jihar Taraba biyo bayan ayyukan 'yan bindiga wanda ya tilasta musu hakura da amfanin gonakinsu.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta sanar da karbo rancen kuɗaɗe har dala miliyan 163 domin bunƙasa noman alkama a ƙasa baki ɗaya. Kashim Shettima ne ya bayyana.
Hukumar Hasashen Yanayi (NiMet) ta ce za a tafka mamakon ruwan sama a Kano da Sakkwato, akasin Ondo, Edo, Delta, Bayelsa, Rivers, Imo, Akwa Ibom, Abia, Ebonyi.
Aikin noma a Najeriya
Samu kari